MUTSAIDA HANKALINMU JAMA'A.MUKARANTA HAR KARSHE!

 MUTSAIDA HANKALINMU JAMA'A.MUKARANTA HAR KARSHE.




ba a hana maulana Amirul wa'izina damar kare kansa ba, kuma babu abunda ya hada tsarin zaman mukabala da zaman kotu kamar yadda wasu suke yaÉ—awa.


Hakikanin abunda ya faru a zaman kotu daya gabata:-


Bayan barister magashi ya gabatar da kudurinsu na janyewa daga bawa malam kariya Alqali sarki yola ya nemi jin ta bakin malam ko yana da tacewa?


Nan take malam yace tabbas yana da tacewa kafin a karbi wannan roko nasu akwai jawabin da yake so nayiwa kotu domin ya shafeta kuma yana da alaka da wannan janyewa tasu.


Anan barister magashi ya nemi kotu ta dakatar da malam daga wannan jawabi tunda ya amince su janye, inda take Alkali ya dakatar dashi da cewa bashi zai faÉ—awa kotu abunda zatai ba, kuma anan kotu ta amince da rokon nasu na janyewar tare da bashi umarnin in yaga dama ya zauna a matsayin É—an kallo in yaga dama ya fice tunda yanzu babu wanda yake wakilta.


Malam ya dora da cewa ya mai girma me shari'a tun sanda naga copy na takardar sabuwar tuhumar da ake akaina nace musu banda matsala da ita ina da amsoshin bayarwa Suka cemun A'a rami ne na mugunta ne aka hakamun 


Malam yace musu to yanzu menene abunyi? Sukace zasu saka kotu ta dawo kan asalin FIR da yan sanda suka gabatar mata, malam yace idan kotu taki amuncewa fa mene mafuta? suka ce sai inyi shiru kada nace uffan, nace musu idan nai hakan babu matsala? 


Suka ce babu wani abu doka ta bani dama, abunda ya fara batan rai akan idanun su da nayi shirun kamar yadda suka umarceni lauyan gwamnati ya tashi yace ga abunda doka ta tanada akan duk wanda aka gabatar masa da tuhuma yayi shiru aje a gwada kwakwalwar sa

Lauyan ya tambayi lauyoyin malam shin kuna da tacewa? Sukace aa sai abunda kotu tace

Daga nan alkalin yayi umarnin duba kwakwalwar malam


Sannan kan mu bar kotu naga su wadannan lauyoy nawa da lauyoyin gwamnatin suna shewa suna dariya a daidai lokacin da ni kuma an cika duniya da cewa kotu ta tambayeni naja bakina nayi shiru ( bisa umarnin lauyoyi)


Malam yaci gaba da cewa Ya mai girma me shari'a duk waÉ—annan kalmomin da ake tuhumata da yinsu bafa tabbatar dasu nake a janibin shugabab halitta SAW ba kore su nakeyi, kuma wannan maudhu'i na auren nana safiyyah maudhu'i ne mai fadin gaske kuma wadannan kalmomi nayi istinbadin su ne daga hadisai 142 haka kuma sai dana duba littafi 94 tsakanin hadisi, sharhi, da lugga


Wannan yasa nace musu banda matsala da wannan tuhuma su bari a karanta ta, suka ce A'a rami aka hakamun yadda akai mun a wajen mukabala haka za aimun a kotu


Ni kuma nasan sashi na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekara ta 1999 sakin layi na 6 ya bada damar a bawa wanda ake kara da “ CAPITAL OFFENCE” cikakkiyar dama ta kare kansa da duk abunda yake ganin zai iya kare kan nasa dashi inda yake cewa:


(Every person who is charged with a criminal offence shall be entitled to be given adequate time and facilities for the preparation of his defence).


Nan take me shari'a sarki yola yayi rubuta bayanin Malam ya É—ago yace malam can wajen sunan sa wajen mukabala nan kuma sunan sa kotu, in sun maka haka acan mu baza muyi maka haka anan ba


Kana da cikakkiyar dama ta kare kanka da duk abunda kake bukata, ka kawo duk wani littafi da kake buta koda zasu cika nan wajan (kotu) ni kawai abunda nake bukata in an gabatar a bani na duba abunda yayimun tsauri zan nemi a barmun in nemi na sama dani su dubamun, in kana bukatar shamela ko wasu bidiyo ko Audio da zaka bawa kotu dan kare kanka duk zaka iya zuwa dasu.


Sannan idan na baka damar magana bazan tsayar dakai ba tun daga safiya har la'asar in baka gama bama daga nan sai mu kara saka wata rana a dawo.


Sai Alkali ya kara bawa Malam dama ya cigaba da bayanin sa, inda Anan barister sa'ida SAN (jagoran lauyoyin gwamnati) ya nemi kotu ta dakatar da waÉ—annan bayanai da malam yake gabatarwa.


Inda nan take Alkali yayi buris da wannan roko nasa Malam ya É—ora da dalilan da yasa lauyoyinsa janyewa waÉ—anda karfinsu kunji a gidajen jaridu:


1-Neman Malam ya Amince a rubuta yana da hauka.

2-karbar kudi a hannunsa da sunan za suyi hira da yan jaridu akan cewa su suka saka malam yin shiru a kotu (kuma basuyi ba) 

3-kokarin kulla alaqa da iyalinsa.

4-labarin da daya daga lauyoyin ya bawa malam na wani masoyinsa ya basu kudi miliyan 15.


Daga waÉ—anda ba kuji a gidajen jaridu ba:


1-Malam ya sanar da Alkali sarki yola karbar kudi da Barister Rabi'u yayi a hannun wani bawan Allah masoyinsa naira miliyan 8 bai Sanar da malam ba sai da suka je da mutumin wajensa 

sannan malam yake sani 


wanda wancen kudin shine kudin da suka caja a shari'o'in malam guda hudu.


2- Malam ya sanar da kotu kudin da suka karba akan zasu karbo order da zata hana a kamashi wanda har zuwa yau da nake gaban kotu babu wani cikakke kuma gamsa shen bayani da sukayi min akan ina wannan order ta makale


3-Malam ya sanar da kotu Rabi'u ya fada masa wani babban jami'in gwamnati ya kirashi yace ya fito ya fadawa duniya an bawa malam isasshen lokaci a wajen mukabala shine kawai bai kare kansa ba zai bashi daga naira miliyan daya har miliyab 100.


Malam yace: bayan an kwana biyu da bani wannan labarin shi Rabi'un yace mun shi wannan jami'in gwamnatin yana son magana dani zai kirani, ya kirani na É—aga yake cemun malam idan har kana son wannan maganar (ta cewa ka zagi Annabi sawa) ta mutu to ka fito ka karyata kanka ka wanke Qaribu daga zargin kisan Liman Malam Aliyul khawass.


4- malam ya fadawa alkali cewa shi daya daga cikin wadannan lauyoyin nasa “rabi'u” shi ya kirashi bayan yin muqabalar wasan kwaikwayo akan lallai sai malam yayi audio na cewa ya  janye wadannan kalamai da ake tuhumarsa dasu kuma ya nemi yafiyar al'umma inda da farko malam yaki yarda sai shi wannan lauya ya daga hankalin wasu daga dattawan da malam yake ganin kimar su akan idan har malam beyi wannan audio ba to lallai zai salwantar da rayuwar sa ne ta tasu rayuwar hakan tasa dole malam badan ya so ba sai dan maslahar mabiyansa yayi wannan audio na minti 4 inda daga baya rabiu yace ba haka suke bukatar sa dole kada wannan audio ya wuce 1min hakan kuwa akayi. 


Duk waÉ—annan suna daga bayanan da malam ya gabatarwa da kotu Ranar 16/09/2021 wanda daga su Alqali Sarki yola ya daga zaman zuwa gobe Alhamis 30/09/2021.


TAMBIHI:


1-yan uwa mu kame bakin mu daga zagin kowa mu cigaba da ruwan Hasbunallahu wani'emal wakilu tare da yiwa shi kansa Alqalin da yake jagorantar wannan shari'ar Adduar Allah ya bashi ikon sauke nauyin da ya dora masa yayi riko da hannunsa wajen yin Adalci a shari'ar.

 Sannan mu cigaba da saka sabbin lauyoyin mu a addu'a suma ubangiji ya karfafe su 


2-muyi watsi da duk wani rahoto da yake nuni da cewa tsarin da akai a wajen mukabala shi za'ai a kotu in mukai haka ba muyi Adalciba tabbas Alqali ya bawa Malam damar kare kansa da isasshen lokaci kamar yadda doka ta bashi sai dai fatan Allah yayi riko da hannunsa ya cika wannan alkawari


BAKIN ALBISHIR GA YAN MAJA.


Maulana Amirul waizina baya neman fita daga wadannan nambobi da kukayi kaidin su kafin ya baku amsa da karfin ikon sarkin da ya baku ikon zakulo wannan da hannunku zaku karbi sakamakonta da hannunku tun daga nan duniya, bawai rashin amsar baku bace tasa shirun akwai amsoshi ba amsa daya ba,


Allah ya baku ikon karbar gaskiya da fahimtar daku hakikar matsalar da take fuskanto ku kuyi gyara tun kan lokaci ya kure muku.


FARIN ALBISHIR GA KHAFAWA:


Ya zama wajibi ga duk wani kahfiy ya kara godiya ga Allah madaukakin sarki da a kullum yake dada tabbatar mana da gaskiyar tafiyar mu 


A da tuhuma 9 suke amma yau gashi da kansu sun zabge 5 tuhuma ta dawo 4 wanda a hakikanin gaskiya 2 ce domin tuhuma 3 farko mas'alace guda 1 suka rabata 3 


Kuma mu kara dagewa da Addu'a ga jagoran namu ubangiji ya cigaba da bashi kariya da kukawa a duk inda yake


Sannan mu ajjiye kunji-kunji mu cigaba da dukufa a kofar sarkin da shi yake mana komai kuma shi yake bamu duk wadannan nasarorin da muke ciki.


Sannan malam ya umarcemu da lalle mu muhimmanta Zikirin Riyadul janna mu karanta Hira da wasanni


Muna Adduar Allah ya taimaki jagora ya kara masa lafiya,juriya da ikilasi yayi riko da hannunsa.

Comments

Post a Comment