CIGABA DA ABINDA YAFARU A KOTU.NA 28/10/2021


ABAN ABINDA YA FARU A KOTU YAU 28/10/2021


L/G a cikin waɗannan shekaru da kake bibiyarsa ko zaka iya tuna ranar 10/8/2021 ?


Shaida:: Eh zan iya 


L/G : to me zaka tuna ?

Shaida: abinda zan iya tunawa a yammacin wannan ranar Juma'a na halacci karatun wanda ake ƙara, a masallacin Ashabul-kahfi, inda a cikin karatun Malam na ji yana cewa ya zo cikin Muslim a hadisi mai lamba 1375 da kuma Hadisi mai lamba1428 cewa, fyaɗe Annabi s.a.w ya yiwa Nana Safiyya bisa daraja ta farko, sannan kuma ƙwacenta ya yi, sannan kuma ya yi mata auren dole. Ya ce ta faɗo a cikin rabon wani mutum....Sai Alkali ya ce masa wane ne wani mutum ? Sai shaida ya ce wani sahabi.

 Shaida sai ya ɗora da Annabi ya ji labarinta sai ya sa aka ƙwato masa ita daga hannun wannan mutum, ya kuma musanya masa ita da kuyangi guda bakwai a madadinta, sai Annabi ya ce mata ki aure ni dole, ƴancinki sadakinki fyaɗe kenan.


Don haka waɗannan kalmomi na ƙwace, da fyaɗe da auren dole tabbas na ji su daga bakin Malam Abduljabbar, domin ina zaune a cikin masallacinsa a lokacin.


L/G: Shin zaka iya tuna ranar 20/12/2019 da kuma 25/10/2019 ?


Shaida: Tabbas zan iya tuna tuna waɗannan ranaku dukansu juma'a ne. Lauya jaddada masa duka Juma'a ne ? Ya ce eh duka Juma'a ne.


L/G: To me ka tuna ?

Shaida: ya ce bisa al'data da nake halartar karatun Malam, a wannan rana malam ya ce akwai Hadisi cikin Bukhari da Muslim Hadisi mai lamba 5120 da Hadisi mai lamba 2324 cewa wata mata ta zo wurin Annabi s.a.w tana yi masa kwarkwasa, sai ta ce masa ya ma'aikin Allah ina sha'awarka. Sai ya ce mata jeki ki samu wani wuri, sai ya zo ya same ta a wani kwararo ya biya mata buƙatar ta.


Sannan a cikin wani karatu Malam yana cewa ya biya mata buƙata ne irin ta ɗa namiji da mace. Wanda waɗannan kalmomi da malam ya ambata na kwarkwasa da sha'awa da sauransu, na ji su da kunne na a bakin wanda ake ƙara.


L/G: wannan abu da ka ce ka ji a ina ne ?

Shaida: a masallacin Ashabul-kahfi ne na wanda ake ƙara.


L/G: shin wacce rana ne aka karatun ?

Shaida: ya ce ranar juma'a a Ashabul-kahfi, ranar Lahadi a sabuwar gandu Jami'urrasul. Wanda a can Gandun ma ya faɗa mana irin wannan magana da na ce na ji.


L/G: waɗancan lambobin Hadisai da ka ce ka ji ya faɗa shin kai ka duba su ne ?

Shaida: ya ce a matsayi na na ɗalibin ilimi da na ji malam ya faɗi waɗancan kalmomi sai na ji basu kwanta mini ba. Hakan ta sa na koma waɗancan litattafai (Bukhari da Muslim) ƙarƙashin waɗancan lambobin Hadisan da ya ambata, sai na tarar babu waɗannan kalamai da ya ambata. To a nan shaida yana ƙoƙarin ci gaba da bayanin cewa shi a mtsayinsa na ɗalibin ilimi.......sai alƙali ya dakatar da shi da cewa ka tsaya a iya abinda aka tambaye ka.


L/G: ya mai girma mai Shari'a iya tambayar da yiwa wannan shaida tamu kenan.


Alkali: ya juyo kan lauyan Malam da cewa to ka ji duk abinda shaidan waɗanda suke ƙara ya faɗa, shin ka yarda da duk abinda ya ce kuwa baka yarda ba ?


L/Malam: ya ce a'a bamu yarda da abinda wannan shaida ya faɗa ba.


Alƙali: Ya ce da lauyan Malam to tunda baka yarda da abinda shaida ya faɗa ba kana so ka yi masa tambaya ne ko suka ?


L/malam: na so na yi tambayoyi, amma kafin nan, zan bawa Ƙanina abokin aiki na Usman dattijo ya yi tambayoyi ga shedar waɗanda suke ƙara.


Alƙali: ya juya ga lauyan Malam, Usman ya ce to ga shedar masu ƙara nan ka yi masa tambaya.


L/malam na biyu: ya tashi ya fara magana cikin barkwanci yake cewa ai shi lauya (lauyan malam na farko kenan) ai ya yi azarɓaɓi, domin ai ba tambaya zamu fara ba tukunna, akwai rokon da muke so mu yi a gaban wannan kotu mai albarka.


Alƙali: ya ce to roƙonku kan wannan shaida ne ko kuma kan abinda ya faru a baya ne, domin idan kan abinda ya gudana a baya ne ba zan baku dama ba, amma idan kan wannan shaida ne ka faɗi roƙon ka.


L/malam na biyu: ya ce eh kan wannan shaida ne.


Alƙali: ya ce to mene ne roƙon naka ?


L/malam na biyu: muna roƙon wannan kotu mai alfarma da ta sahhalewa shi Malam Abduljabbar ya yiwa wannan shaida tambayoyi har ma da suka da kansa. Kuma muna da hujjoji da zamu gabatar a nan gaba na cancantar hakan wanda zamu gabatar da su a nan gaba, amma a yanzu muna roƙon kotu da sahhalewa Malam Abduljabbar, da fatan kotu zata karɓi roƙonmu.


Alƙali: ya ce to mu duk abinda zamu yi muna dogaro ne da nassi ko doka, saboda haka tunda ka nemi mu sahhalewa wanda ake ƙara ya yi tambayoyi da suka da kansa ga shaidan wadanda suke ƙara, to ya zama wajibi ka bamu hujjar da ya ce a yi hakan. Ba wai na bashi dama ba yanzu sannan daga baya a kawo hujja, wannan ya saɓa da Shari'a, don haka mene ne kuka dogara da shi ?


L/malam na biyu: ya ce ina roƙon kotu ta bani rana na zo mata da hujjojin da suka ce a yi hakan (ma'ana a ɗaga zama zuwa gaba).


Alƙali: ya juya ga lauyan Gwamnati ya ce ka ji abinda ya faɗa da kuma rokon da ya yi, ko ka amince ?


L/G: ya ce mu dai bamu da suka, kan cewa a bawa wanda ake ƙara ya yi tambayoyi da suka ga shaida, bisa la'akari da wata doka da ya faɗo, amma fa idan ya yi tambayoyi da suka su kuma lauyoyinsa ba zasu yi ba.


Alƙali: ya juya ga lauyan malam to ka ji abinda lauyan Gwamnati ya faɗa, ya ma goyu da bayanka, shin ka amince da abinda ya faɗa ya zama hujjar ka, ni kuma na faɗi matsayi na ko kuma ka fi so a ɗaga maka ɗin ?


L/malam na biyu: ya ce eh na yarda ba sai an ɗaga mini ba, wannan abu da aka faɗa a bawa malam Abduljabbar ya yi tambayoyi da sukar da kansa mu kuma ba zamu yi magana ba, na amince da wannan sashi.


A daidai wannan lokaci Alkali ya bayar da damar tafiya hutu na taƙaitaccen lokaci.

_____________


Bayan an dawo wannan hutu Alkali ya mayar da kanun abinda ya faru na ƙarshe kafin tafiya hutu.


 Nan take ya bayyana rashin amincewarsa na bawa malam dama ya yi tambayoyi da suka ga shaidar waɗanda suke ƙara, amma fa ya ce a fahimtarsa duk da ya ce akwai abinda ya dogara da shi a cikin dokar da lauyan Gwamnati ya faɗo na bayar da wannan dama ga malam Abduljabbar.


 A daidai wannan lokaci malam Abduljabbar ya ɗaga hannu alamar yana son ya ce wani abu, nan Alkali ya bashi dama da ya yi magana.


M/Abduljabbar: ya fara da cewa ina neman afuwa zan yi magana ba tare da mun tattauna da lauyoyi na ba, tun daga ranar da aka gurfanar da ni a wannan kotu har zuwa zaman da ya gabata a cikin biyayya ga lauyoyi nake. Wanda cikin wannan biyayya ne ta sa a gaban kowa na zo nan wurin ka yi mini magana amma na yi maka shiru, domin bin umarnin lauyoyi na (ina nufin sa'ilin da aka yi mini magana na yi shiru).


Malam ya ɗora da, kuma na tambaye su hujjar yin hakan, amma basu bani wata hujja gamsasshiya ba, amma a hakan na yi ladabi garesu na bi umarninsu gareni. Wanda har suke faɗa min cewa an shirya min makirci ne irin wanda aka shirya min a wurin Muƙabala. Kuma na tambaye su yin shirun da kuka ce na yi babu wata matsala ?

 Suka ce mini babu wata matsala.

 Na yi biyayya gare su, a nan wurin a gaban kowa ka yi magana da ni, na yi maka shiru duk don biyayya garesu, a ƙarshe dai sai na ji saɓanin abinda muka tattauna da su a prison. Wanda ta kaini ga zama Mahaukaci, ba don Allah ya Laɗɗafa mini ba da tuni duk abinda na assasa ya rushe gabaki ɗaya.


Kuma ni tun a ranar da aka kawo wannan tuhuma ina da amsoshinsu, shi ya sa ma na yi musu alkawarin ba zan ƙara yin shiru ba. Kuma duk a cikin yi musu biyayya abubuwa da yawa sun faru wanda a ciki har da na keta alfarmar iyali na, wasu na iya faɗarsu wasu kuma na barwa Allah ya yi mini sakayya. Kuma ko waɗancan lauyoyin ni bamu magana da su zasu janye ba, kawai da muka zo kotu ne nake ji daga garesu sun janye.


Kuma yanzu fa bayan waɗannan litattafan na gaba na akwai wasu a cikin mota sama da guda ɗari 100 wanda duk suke magana a kan waɗannan kalmomi da ake magana a kan su. Kuma duk lokacin da na yi irin waɗannan karatu wasu ne fa suke sukar Annabi da irin waɗannan Hadisai, kuma ina da shaida wanda ko yanzu kotu ta buƙata zan danna recorder don a ji misalan irin yadda ake ɓata Annabi da irin waɗannan Hadisai, kuma har ta kai ga an ƙure mai kare Annabin s.a.w. Ni kuma shi ne nake karatu na kare Manzon Allah na kore Hadisan da basu tabbata ba, wanda kuma basu gane ba na fahimtar da su yadda abin yake.


Alƙali: ya ƙara jaddadawa malam sai dai fa lauyoyi su yi magana kai ka haƙura ko kuma ka sallami lauyoyinka ka kare kanka da kanka.


M/Abduljabbar: ya ce to yanzu idan lauyoyi suka gaza bijiro da hujjoji na ya za'a yi kenan ? Malam Abduljabbar ya ɗora da cewa ni ba hukuncinku nake tsoro ba, illa ɓata mini suna da kuma kallafa min abin da ban aikata ba, domin ni kare ma'aikin Allah nake yi ba ɓata shi ba. Duk lokacin da na yi karatu wasu ne suke ɓata shi ni kuma nake kareshi.


Abinda nake son faɗa rigimar nan fa duk a kan aure Nana Safiyya ne, wanda duka waɗannan litattafai da nake tare da su suna ɗauke da wannan mas'alar. Malam Abduljabbar ya ɗora da cewar ko mun zauna da lauyoyi na ko bamu zauna ba, ba fa zasu iya faɗar waɗannan hujjojin nawa ba.


Domin a prison na bawa lauyana sharhin da aka yi fassara irin tawa, amma ya kasa karanta bakin ballantana fassara. Don haka kowa da abinda ya ƙware a kai, ni shari'a ta magana ce ta Hadisai ba magana ce ta Low ba.


Malam Abduljabbar ya ɗora da cewa kuma mun samu matsaya har da yarjejeniya da lauyoyi na cewa idan an zo kotu zan bijirar da tambayoyi na, ga takardar ya mai Shari'a, Alkali ya ce ajiye takardar ka malam na ganta. Kuma ya nemi da har wancan shaidar a dawo da shi, domin duk abubuwan da suke faɗa juyamin zance suke yi, ni ba haka na ce ba za'a iya ɗakko murya ta a danna a ji me nake nufi, hatta shi wancan shaidar da yake maganar shi ba malami bane jahili ne, ni dai ban taɓa jin inda jahili ya haddace Ƙur'ani izu 60, sannan ya haddace litattafan Hadisai 20, litattafan fikihu 10, litattafan Tauhidi 10 ba, kuma ya matsa gaba ya ce kakaf litattafan musulunci babu inda aka yi wannan fassara tawa wannan yake kenan ya karance su duka, ka ga kuwa wannan ba jahili bane don haka a dawo da shi, shi ma ina da tambayoyin da zan yi masa.


Kuma ina ƙara faɗa duk shawarwarin da Alkali ya bani na bisu, kuma ina so a fahimta cewa wannan fa maganar ba ƙaramar matsala ba ce, ya kamata na bijirar da Hadisan nan kowa ya gani.


Idan kuwa ya zama lallai babu makawa sai na sallami lauyoyi na sannan zan bijiro da waɗannan hujjoji to kuwa lalle na haƙura da lauyoyi na, na dogara da Allah, su je su ci gaba da yi min sauran shari'u na. Tun da hakan ya zama ba makawa sai an haƙura da su sannan zan iya kare kaina.


A daidai nan lauyan Gwamnati ya yi suka cewar an bar shi yana ta bayanai.

 

Alkali: Sai Alkali ya ce a'a ai dole a bashi dama ya yi bayaninsa.

 Lauyan.


 L/G: sai lauyan Gwamnati ya ce to ai Malam depence yake yi.


Alƙali: ai ba depence zai yi ba, idan ma depence ɗin zai yi zan dawo da shi kan hanya.


L/G: ya ce ai zai iya yin tambayoyinsa da kuma suka kuma lauyoyinsa suna cikin Shari'ar, ya ɗora da cewar irin wannan tuhumar wacce idan ta tabbata hukuncin kisa ne ai ba'a yin ta babu lauya. Don haka muke roƙon kotu ta bamu dama mu je mu tattauna mu zo mata da matsaya....sai Alkali ya ce idan na amince ? Sai lauyoyi suka gyara da ko kotu zata amince. Nan Alkali ya ɗora da cewar ba laifi bane don Alkali ya yi gyara bisa hukuncin da yake ganin akwai kuskure a cikinsa. Yin hakan ba laifi bane.


Take Alkali ya basu damar zuwa wannan tattaunawa. 

 Sai kuma lauyan Gwamnati ya nemi a ɗaga wannan ƙara don samun damar wannan tattaunawa, haka kuwa aka yi Alkali ya ɗage Shari'a zuwa mako biyu masu zuwa.


Allah ta'ala ya datar da mu Duniya da Lahira, daga ni Ɗan uwanku a Allah.

©Fatimiyya Alawuyya Tv

Comments