LAUYOYIN SHEIKH ABDULJABBAR SUNNEMI BELINSA A KOTU YAU 25/11/2021

LAUYOYIN SHEIKH ABDULJABBAR SUN NEMI BELINSA A KOTU

Daga
 Aliyu Samba



A yau ne babbar kotun shari'ar Muslunci ta Alƙali Ibrahim Sarki Yola dake zamanta a kofar kudu a birnin Kano ta cigaba da saurarar shari'ar Malamin Addinin musulunci Sheikh Abdujabbar Kabara bisa zargin sa da Kalaman ɓatanci da tunzura jama'a. 


 


A zaman shari'ar da ya gabata, kotun ta nemi da a kawo wa Malamin Kwafin Littafin Bukhari da Muslim daga jami'ar Bayero dake Kano, wanda aka fara zaman na yau da gabatar da wadannan littafai ga kotu. Sannan kuma kotu ta tambayi Malamin ko an bashi kudin siyan littafan kaman yadda aka fada a zaman da ya gabata, malamin ya tabbatar da cewa an bashi kuma ya siya, sannan yayi godiya.


 


A zaman na yau Malamin ya cigaba da tambayoyi ga shedar, inda a ciki ya tuhumi shedar da canza masa magana.


 


''Shin ya halatta sheda ya canzawa Wanda ake ƙara lafazin sa?'' inji malam Abdujabbar


 


Shedar bai amsa tambayar da eh ko a'a ba, saidai yace ''Ni na faɗi iya abinda kunne na ya jiye mun ne daga bakin ka"


 


Malamin ya sake tambayar shedar ''Yanzu da zan kunna karatun nan aji ya saba da shedar daka bayar, menene matsayin shedar ka?"


 

ya

''Matsayin sheda ta hurumi ne na kotu" inji shedar. 


 


Malamin ya tuhumi shedar da cewa iƙirarin sa na ɗalibta a gareshi ba gaskiya bane, inda ya soki shedar da wasu rubuce rubuce da yayi a shafin sa na facebook tsawon shekaru, yana wallafa kalaman ɓatanci akan sa. 


 


Malamin yayi jan hankali ga kotu cewa batayi "Tahququl Da'awa" ba kafin sauraren sheda, saidai kotun ta yi masa bayanin cewa anyi, kuma damar da aka basu a baya shine baiyi maganar ba. 


 


A sukar da Malamin yayi, ya kawo wani littafin da shedar ya taba rubuta masa raddi akan ingancin sunayen Allah da suke cikin littafin dala'ilul Khairati, inda malamin ya karanto cewa shedar a shafi na 2 cikin littafin, ya ambace shi da Mulhidi, dan bidi'a, mai wuce gona da iri a sufanci, sannan kuma wanda ya taso a tsatson yan bidi'a.


 


Ya bayyana wa kotu cewa wannan shedar maƙiyin sa ne, kuma ba gaskiya ya fada a kotu ba na danganta kansa da ɗalibta gareshi, da kuma cewa da yayi Yana shiga ajin su a lokacin da shedar yace yana karatu a makarantar Ma'ahad Sheikh Nasir Kabara dake Gwale. Ya kuma nuna wa kotu rubuce rubucen da shedar yayi sama da shekaru 7 yana ambatar sa da sunaye marasa dadi, da kuma inda aka rubuta a shafin sa cewa shi ma'aikacin kungiyar izala ne (JIBWIS), Malamin ya yi zargin cewa wannan sheda bazai taba fadar gaskiya akan sa ba. 


 


A nasa bangaren, shedar ya gayawa kotu cewa kimanin wata biyu ya samu wata yar matsala da shafin sa na facebook inda yaga an sauya masa abubuwan da ya rubuta. ''Ina kyautata zaton wannan JIBWIS da aka saka, a lokacin da aka mun kutse ne, amma Ni ba dan kungiyar JIBWIS Bane'' inji shedar. 


 


Lawyan Wanda ke gabatar da ƙara Barista Sa'ida SAN ya nemi kotu da ta bawa abokin aikin sa Barista Yakubu Abdullahi damar yayi jawabi akan sukar da Malamin yayi, kotu ta bashi dama. 


 


''Wannan suka da wanda ake ƙara yayi wa sheda, idan an dube su ta ɓangaren doka da Shari'a ba abin karɓa bane, idan akayi la'akari da sashi na 175 karamin sashi na 1 na Evidence Act 2011'' inji Yakubu


 


Lawyan Wanda ake ƙara ya roki kotu da ta bashi dama yayi martani akan sukar da Lawya mai gabatar da ƙara yayi, kotun tace, ta bashi dama shine abinda ya fi kusa da adalci.


 


''A cikin Tuhfa shafi na 48, an kawo cewa a shari'ar Musulunci ba a karbar sheda da Evidence Act, mai sheda ga dan uwansa sai ya zamo mubarrizi wanda shi wannan shedar ba mubarrizi bane ba'' Inji Lawyan wanda ake ƙara.


 


Ya ƙara da cewa ''Kotun ɗaukaka ƙara tace baza a karɓi sheda ba sai daga musulmi, Baligi, Adali, kuma ya zama babu ƙiyayya tsakanin sa da wanda ake ƙara, kuma ya zama ba abokin sa ba''


 


Ya kuma kara da bayyanawa kotu cewa Lawyoyi masu gabatar da ƙara sunyi coge a nassin da suka kawo cikin littafin ''Fawakihuddawani'' na cewa ba a karbar shedar abokin husuma. A ƙarshe ya roki kotu da ta yi watsi da wannan sheda. 


 


Alƙali Ibrahim Sarki Yola yace dukkan lawyoyin sun fadi hujjojin su da doka da nassi, kuma zai nazarce su sannan ya fadi matsayin wannan sheda a gaba. 


 


Saidai kafin a ƙarƙare zaman na yau, Lawyoyin wanda ake ƙara sun sake rokon kotu da ta bada belin wanda ake ƙara da sharadi, duba da Matsayinsa bazai ketare sharadin ba, kuma zai zo kotu a duk sanda aka buƙata.


 


Kotun tace zata duba, idan taga dacewar hakan zata bayar da shi beli. An daga karar zuwa 9 ga watan Disamba, 2021 dan sauraren sheda na 3. 


 


©Fatimiyya Alawuyya Tv 


25/11/2021

Comments