GANDUJE YAKAIWA KWANKWASO ZIYARA HAR GIDA

 GWAMNA GANDUJE YAJE TA'AZIYYA WA KWANKWASO,

GWAMNA GANDUJE YAKAI WA KWAN KWASO ZIYARA NA TA'AZIYYA HAR GIDANSA,


Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya je yi wa tsohon gwamna kuma babban abokin hamayyarsa Rabiu Musa Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar É—an uwansa.

Gwamnan ya isa gidan Kwankwaso na Miller Road da tsakar ranar yau Talata, inda suka ziyarci ƙabarin mahaifin Kwankwaso da ya rasu a baya.

A ranar Litinin ne Inuwa Musa Kwankwaso, wanda ƙani ne ga Rabiu, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Ya rasu yana da shekara 64.

Alaƙa tsakanin shugabannin biyu ta daɗe da lalacewa tun bayan da Kwankwaso ya miƙa wa Ganduje ragamar mulkin Kano a 2015 bayan sun shafe shekara takwas a matsayin gwamna da mataimaki. har ta kai ga yanzu Kwankwaso ya koma jam'iyyar adawa ta PDP.

Sai dai Gwamna Ganduje na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida a jam'iyyarsu ta APC tsakaninsa tawagar tsohon gwamna kuma sanata a yanzu, Malam Ibrahim Shekarau


©Fatimiyyaa

Comments