Banban cin halinda yake ciki da na sauran mala man maja. Daga wani bawan Allah
Mahmoud labaran Galadanci.
Na sha fadawa mutane a hira, Dr. Abduljabbar a zahiri ne yake a kulle amma a bude yake da cikakken 'yanci. Rufaffen mutum shi ne wanda ya hana kansa 'yancin tunani da zabi a rayuwarsa musamman a addini.
Dr. Abduljabbar ya bawa kansa 'yanci cikakke wadanda suka masa sharrin kuma tunaninsu a rufe yake, a hakika su ne a rufe.
Har inda yau take basu yadda sun yi nasara a kansa ba kuma wannan ranar ba zata taba zuwa ba. Kullum nasara yake kirgawa babu ranar da zai fadi. Sannan tarihi ba zai taba mantawa dashi ba don ya ajiye jijiyar da har jikokin mu ba zata gushe ba.
Ban taba karanta tarihin wani wanda a yau ake neman albarkarsa ba da bai shiga yanayin da Malam Abduljabbar ya shiga ba a yau.
Dukkan limaman mazhabobin da ake addini da fahimtarsu suna da irin wannan tarihin.
Haka ma wadanda Allah yafi so yafi kauna bayan manzon Allah, Ahlin gidansa, duk sun shiga wannan yanayi. Yau dasu muke kamun kafa. Shi ma ku rubuta ku ajiye, Allah ya bamu tsawon kwanaki.
©Fatimiyyaa
Comments
Post a Comment