Fassaran Kasidar sheikh Abduljabbar,


 FASSARAR KASIDAR (LASAIFA  ILLA ZUL FIQARI)TA MAULANA AMIRUL-WA,IZEENA SHEIKH ABDULJABBARA KABARA                        (HAFIZAHULLAHU)


1-لاسيف إلا ذوالفقار

ولا فتى إلا علي

Bawata takobi sai zulfakari ba wani jarumi sai Ali


2-وابن الربيعة عتبة

نادى فزلزله علي

Dan rabee'ah wato utbatu bin rabee'ah yayi shelar wazai kara dashi sai imamu Ali  ya girgizashi


3-وكذاك خرطوم الولي 

دماه بدر في علي

Hakanan waleedu bin mugeerah Imamu Aline yayi jina jina da zozon hancinsa  a ranar yakin badar ma,ana  yayi kasa-kasa dashi kamar yadda Allah ya fada cewa

( سنسمه على الخرطوم) 

To imamu aliyune ya cika wannan alkawari.


4-من بعد حمزة جا عبيدة 

كان أولهم علي 


Bayan   jarmai hamza Dan Abdul muttalib,  ubaidatu binil harith wato Dan baffan shugaba yazo,Amma  Wanda yazamo na FARKO shine imamu Ali wato aranar badar lokacin da za,ayi mubaraza kafin fara yaki.


5-ومن الذي في يوم أحد 

جز طلحة  قل علي 

 Wane a ranar  yakin uhudu ya datse  kan dalhatu bin dalha  kace aliyune yakai mai sauraro.

.

6-وكذا ابن ود يوم خندق

لم يجبه سوى علي

Haka zalika ranar yakin khandaku(gwalalo) da amru bin abdi wuddi  yayi shela ya cika kuri wazai kara dashi ,babu  Wanda ya amsa masa  inba imamu Aliyyuba.


7-ولواء خيبر جازه 

هذا وذاك بلا علي

Tutar  yakin khaibara  wane dawane sun karbeta akaran farko wato( Abubakar da umar) ba Aliyuba.


8-فإذا اليهود تغلبوا 

إذ لم يبارزه  علي

A lokacin da yahudawa sukai  nasara saboda Aliyu baiyi futo na futo dasuba.


9-قال النبي غدا أسلم

ذا اللواء إلى علي

Sai Annabi yace gobene zan sallama wannan tuta izuwa Aliyyu.


10-لن أعط فرارا غدا

أعطيه فرارا علي

Agobe bazan bada tuta ga Wanda ake koroshiba,zan bada itane ga dirkakau Wanda yake kai hari ba tare da juyawaba wato imamu Ali.


11-عبد يحب الله ثم 

رسوله يدعى علي

Shi bawane Wanda ya ke kaunar Allah ya ke kaunar manzansa Wanda ake kira da ALIYYU.

 

12-والله كان يحبه

ورسوله يهوى علي

Allah yana kaunarsa kuma  manzan Allah ma yana kaunar imamu ALI.


Wannan nunine zuwa ga hadisin khaibara Wanda ciki Annabi (saw) yake fada:

(لأعطين الراية غدا رجلا يفتح على يديه يحب الله ورسوله ويحبه الله ورسوله)


13-لما خبت نيرانهم

في الحرب أججها علي

Yayinda wutar yakinsu ta bice imamu ALIYYU ne ya rurata .


14-لما تأخلج قوسهم

في الرمي سدده علي 

Yayinda kibiyarsu ta karkace wa saiti  ta baude a wurin harbi to  Aliyyu ne ya katartar da ita wato yasaitata.


15-ولواؤهم لما تأرجح

ظل يرفعه علي

Tutar suma lokacinda take walawala kamar zata fado  ALIYYU ne yazo ya dagata.


16-نعم الشجاعة حبذا 

حييت مولانا علي 

Madallah da wannan sadaukanta  angaisheka ya  maulana  ALI.


17-نفديك بالأرواح والأموا

ل سيدنا علي 

Fansan rayukanmu da dukiyoyinmu agareka ya sayyidana ALIYU.


18-من كان سيده النبي 

فإن سيده علي 

Duk Wanda Annabi yake  shugabansa to Imamu Aliyyu ma shugansane.


19-من كان قائده النبي 

فإن قائده علي

Duk Wanda  Annabi yake  jagoransa to Aliyyu ma jagoransane.


20-من كان مولاه النبي 

وليه حقا علي 

Duk Wanda Annabi yake abun jibantarsa wato shugansa to aliyyuma tabbas abun jibantarsa ne kuma shugansane.


kamar yadda shugaba ya fada acikin hadisi:

( من كنت مولاه فهذا علي مولاه)


21-بعد النبي ولي كل 

المؤمنين غدا علي

Bayan wafatin ma,aiki to ALIYYU ya zama shine majibuncin dukkan muminai. Kamar yadda umar bin khaddabi ya fada a bayan Annabi ya gama bayyana hakan a ranar (gadiru khummin) cewa:

(بخ بخ لك يا ابن أبي طالب لقد أصبحت مولاي ومولى كل مؤمن.....)


22-للهم وال مواليا 

بالحق قد والى علي 

Ya ubangiji ka jibinci wanda ya jibinci  lamarin imanu ALIYYU da gaskiya.


23-للهم عاد معاديا 

بالبغي قد عادى علي

Allah kayi futo na futo da Wanda yayi futo na futo da imamu ALIYYU da zalunci wato(fi,atul bagiya) da wasunsu.

Wannan addu,ar Annabi (saw) ce  inda yake fada acikin hadisi a hakkin imamu ALIYU: 

(اللهم وال من والاه وعاد من عاداه)


24-واجعل لنا في الحوض

حظا حين يحرسه علي 

Ka sanya mana rabo daga tafkin alkausara alokacin da imamu ALIYYU yake gadinsa.

Kamar yadda ya tabbata a riwaya daga bakin imamu hassan Dan Nana fadima  cewa sayyadi aliyyu shine zai zama yana gadin tafki yana korar  munafukai daga shansa, ranar tashin alkiyama.


25-أبعد أولى قد بدلوا 

عنا ومن كرهوا علي 

Allah ka nesata wadanda suka canza a bayan ma,aiki daga garemu da kuma Wanda suka ki Aliyyu (wato wadanda za,a kora daga sahabbai daga tafki,har Annabi saw zaice sahabbai nane fa sai ace masa( hakika sun canza a bayanka sai yace to ayi nesa dasu.)

(إنهم قد بدلوا بعدك)


26-ثم الصلاة على النبي 

وآل فاطمه من علي

Ya Allah kayi salati ga Annabi da iyalan  sayyida fadima yayan  imam Aliyyu wato Ahlulkisa'i.


27-حسن حسين زينب 

من بعد فاطمة علي 

Sune imamu hasanul MUJTABA da imamu AbuAbdillahi Alhusainu, da sayyida zainabul kubra, bayan sayyida fadima da imamu ALIYYU.

Wadannan sune ahlin ma,aiki (saw) da zuriyarsu.


ما هام ذا عبد لجبار 

ينادي يا علي

Allah kayi wannan salati duk sanda wannan bawa naka mai suna ( ABDULJABBAR) ya dimauce saboda kaunarsu alhali yana yekuwa yana cewa: YA ALI! YA ALI!


Fassara daga 

-Faisal Aminu umar R/Lemo

- Muhyiddeen Ahmad Sharif Daga Mujamma'u As'habil Kahfi Warraqeem Kano Nigeria. 

20/02/2022

Comments